Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci a samu daidaito tsakanin bada kariya daga annobar COVID-19 da matakan rage illar cutar ga zaman rayuwar al'umma
2020-06-23 10:56:45        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci a samu daidaito tsakanin bada kariya daga annobar COVID-19 da kuma takaita illolin da cutar ke haifarwa tattalin arziki da yanayin zaman rayuwar al'umma, yayin da adadin sabbin masu kamuwa da cutar ke kara yawa a kullum a sassan duniya.

"Ba zai taba zama zabi ne tsakanin rayuwa ko kuma zaman rayuwar al'umma ba. Kasashen duniya za su iya hada duka biyun," babban daraktan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana hakan, ya ce dukkan kasashe na cikin wani yanayi na tsaka mai wuya game da batun baiwa jama'arsu kariya, a hannu guda kuma rage tasirin annobar kan zaman rayuwa da tattalin arziki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China