Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni wajen tinkarar bala'in ambaliyar ruwa a cikin kasar
2020-06-28 20:47:14        cri

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni wajen tinkarar bala'in ambaliyar ruwa a cikin kasar, ya ce, tun farkon watan Yuni, wurare da dama na fama da ambaliyar ruwa, hukumomin wurare daban-daban sun yi iyakacin kokarin tabbatar da tsare-tsare da manufofin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, don tinkarar bala'in da ceton mutane, sun samu ci gaba sosai.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya ce, yankuna da hukumomi daban-daban sun nace ga mai da muradun jama'a da rayuwar jama'a a gaban kome, don kokarin tinkarar bala'in, da ba da tabbaci ga rayuwar jama'a. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China