Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu ta samu adadi mafi yawa na masu kamuwa da COVID-19
2020-06-28 16:24:26        cri
A ranar Asabar kasar Afrika ta kudu ta bada rahoton samun sabbin mutane 7,210 da suka kamu da cutar COVID-19 cikin sa'o'i 24, wannan shi ne adadi mafi yawa da kasar ta taba samu na masu kamuwa da cutar a kwana guda, tun bayan bullar annobar a kasar a farkon watan Maris.

Idan an hada sabbin alkaluman, jimillar adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar a kasar ya kai 131,800, hukumar lafiyar kasar ce ta sanar da hakan cikin rahoton da ta saba fitarwa a kullum.

Bugu da kari, hukumar lafiyar kasar ta sake samun sabbin mutanen da cutar ta hallaka 73, wanda shi ya kawo adadin mutanen da cutar ta kashe a kasar zuwa 2,413.

Lardin yammacin Cape shi ne inda annobar ta fi kamari inda aka samu kimanin mutane 59,315 sun kamu da cutar, sai yankin Gauteng dake bi masa baya da jimillar mutane 34,285, sai kuma yankin gabashin Cape mai adadin mutane 23,658 da suka kamu da cutar.

A wani labarin kuma, annobar ta kara hauhawa a kasar ne a makarantu bayan da aka bude makarantun kasar 'yan mataki na 7 zuwa matakin aji na 12 wadanda aka bude a ranar 8 ga watan Yuni. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China