Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayayyakin tallafin yakar COVID 19 da Sin ta baiwa Masar sun isa birnin Alkahira
2020-06-23 10:44:24        cri

Kwanan baya, kayayyakin tallafin yakar COVID 19 da kwamitin kayyade ilyali na kasar Sin ya samarwa kasar Masar sun isa birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar.

Wadannan kayayyakin sun kunshi marufin baki da hanci na aikin likitanci dubu 110, da rigunan kandagarki 1000, da kuma na'urorin gwada zafin jiki da dai sauransu, kuma za a ba ma'aikatar lafiya ta kasar, da kwamiti mai kula da iyalai na kasar Masar kayayyakin ta hannun asusun "Jama'ar Masar", don tallafawa gwamnati, da kuma jama'ar Masar yakar cutar COVID 19. An ce, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta baiwa kasar kayayyakin tallafi har sau uku.

Alkaluman na nuna cewa, a jiya Litinin, yawan sabbin mutanen da cutar ta harba ya kai 1576, inda ake cikin lokaci na saurin samun karuwar mutane masu kamuwa da cutar. Ya zuwa daren ranar jiya, yawan mutanen da cutar ta harba a kasar ya kai 56809, adadin da ya kai matsayi na 25 a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China