Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Angola tana fatan kara hadin kai da kasar Sin wajen yakar COVID-19
2020-06-23 10:51:13        cri
Jiya Litinin, jakadan Sin dake kasar Angola Gong Tao, ya gana da ministar kiwon lafiya na kasar Silvia Lutucuta, inda suka yi musanyar ra'ayi kan hadin kan kasashen biyu wajen yakar COVID-19.

Silvia Lutucuta, ta nuna godiya matuka ga taimakon da Sin take baiwa kasarta wajen yaki da cutar, kuma a cewarta, gwamnatin kasar ta riga ta kafa wasu hukumomin jiyya masu hazaka na yaki da cutar, kana Sinawa dake kasar idan da bukata, suna iya neman taimako daga wadannan hukumomi. A hannu guda Angola za ta yi iyakacin kokarin kula da lafiya da kuma tsaronsu.

Jami'ar ta kara da cewa, Angola na da imanin hana yaduwar cutar, kuma tana fatan zurfafa hadin kai da kasar Sin wajen yakar cutar. Ban da wannan kuma, tana mai fatan kasar Sin za ta ba da taimako, wajen kara karfinta na gwada cutar, da jiyyar wadanda ke harbuwa da cutar.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China