Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani:Akwai fargabar yadda ake kara samun sabbin masu kamuwa da COVID-19 a Afirka
2020-06-15 10:08:52        cri
Mashawarci kan zamantakewa da tattalin arziki a kungiyar tarayyar Afirka (AU) da hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (ECA) Constantinos Bt Costantinos, ya bayyana fargaba kan yadda ake samun karuwar sabbin masu kamuwa da COVID-19 a nahiyar Afirka.

Jami'in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yadda sabbin masu kamuwa da cutar ke bazuwa cikin sauri, abin damuwa ne matuka, duba da yadda wasu kasashen nahiyar ke zama wuraren da aka fi samun yawan sabbin masu kamuwa da cutar ta COVID-19.

Shi ma darektan ofishin MDD mai kula da shiyyar Afirka ta tsakiya Antonio Pedro, kira ya yi ga kasashen duniya, da su taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da wannan annoba. A cewarsa ta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa da taimakon juna ne kadai za a iya yakar kwayar cutar.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, Pedro ya ce, hadin gwiwar kasa da kasa kan COVID-19, abu ne mai muhimmanci, saboda muddin muka gaza magance wannan annoba a Afirka, hakika za ta addabi duniya baki daya.

Bugu da kari darektan ya jaddada cewa, hadin gwiwar kasa da kasa kan wannan annoba, ya wuce tasiri na gajeren lokaci wajen warkar da wadanda suka kamu da cutar, tare da tabbatar da cewa, karin wasu mutanen ba su harbu ba, sai ma a kara inganta daukar matakai. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China