Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan lafiyar Ghana ya kamu da COVID-19
2020-06-15 10:33:30        cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya sanar cewa, ministan lafiyar kasar Kwaku Agyemang-Manu ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Cikin jawabinsa na baya bayan nan da ya gabatarwa jama'ar kasar game da yaki da annobar COVID-19, Akufo-Addo ya ce, "Zan yi amfani da wannan damar domin yiwa hazikin ministan lafiya Kwaku Agyemang-Manu, fatan samun lafiya cikin hanzari daga annobar da ya kamu da ita a lokacin da yake bakin aikinsa".

Ministan lafiyar, wanda ya sha jagorantar taron wayar da kan al'umma game da daukar matakan kandagarkin cutar, ya kasance babban jami'in gwamnatin kasar Ghana a baya bayan nan da aka gwada shi yana dauke da kwayar cutar ta COVID-19.

Shugaban na Ghana ya kuma sanar da mutuwar Kobina Sam, magajin garin Sekondi-Takoradi, bayan ya sha fama da jinyar cutar ta COVID-19.

Ya zuwa daren Lahadi, adadin masu dauke da cutar COVID-19 a kasar Ghana ya kai 11,964, yayin da mutane 54 suka mutu a sanadiyyar cutar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China