Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa dandalin samar da bayanan COVID-19 ga yan Afrika miliyan 600
2020-06-24 11:03:02        cri
A ranar Talata an kaddamar da wani dandalin samar da bayanan lafiyar al'umma irinsa na farko wanda zai dinga samar da sabbin bayanan shawarwari ga mutanen Afrika kusan miliyan 600, musamman game da batun annobar COVID-19 da ake fama da ita a halin yanzu.

Dandalin samar da bayanan na Afrika, an samar da shi ne karkashin hadin gwiwar hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD ECA, da hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC, da kuma mayan kamfanonin sadarwa na kasashen Afrika.

A cewar ECA, tsarin samar da bayanan da aka kaddamar na tafi da gidanka zai dinga samar da muhimman bayanai a matakin kasa da na shiyya game da annobar COVID-19 wanda zai dinga bayyana alkaluma game da halin da ake ciki a matakan kiwon lafiya da tatttalin arziki.

Sabon tsarin wanda zai gudanar da ayyukansa kyauta ta hanyar wayoyin hannu, zai dinga samar da rubutattun sakonni da bayanan murya.

A bangaren babbar fasahar sadarwa kuwa, dandalin zai dinga samar da alkaluma ga al'umma ta hanyoyin intanet da shafukan sada zumunta na zamani.

Kashin farko na tsarin, zai fara aiki ne a ranar Talata, zai baiwa masu mu'amala da wayoyin hannu damar samun bayanan a kasashen Afrika sama da 23, wanda ya kunshi kashi 80 bisa 100 masu ta'ammalai da wayoyin hannu na kasashen Afrika. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China