Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakiyar firaministan kasar Sin ta jaddada bukatar dakile yaduwar COVID-19 a Beijing
2020-06-15 10:16:21        cri
Mataimakiyar firaministan kasar Sin, Sun Chunlan, ta yi kira da a dauki managartan matakai na hada yaduwar cutar COVID-19 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Madam Sun ta yi wannan kira ne, jiya Lahadi yayin taron hadin gwiwa na majalisar gudanarwa da yaki da cutar COVID-19.

Ta ce, sabbin mutanen da suka kamu da cutar a Beijing, na da nasaba da kasuwar Xinfadi, inda mutane da dama ke taruwa, kuma ke cinikin amfanin gona da na ruwa kowace rana, a don haka ta yi gargadin hadarin yada kwayar cutar, tare da yi kira da a dauki matakan dakile cutar.

Jami'ar ta kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan yanayin yaduwar cututtuka a kewayen kasuwar da gano da ma dakile yadda cutar ta samo asali.

Ta kuma jaddada bukatar yin gwajin makwoshi a dukkan muhimman sassan birnin Beijing da kara fadada yin gwaje-gwaje, don gano wadanda suka kamu da cutar da ma wadanda ba sa nuna alamun kamuwa da cutar.

Madam Sun ta kuma yi kira ga jama'a, da su dauki matakan da suka dace na kandagarki da hana yaduwar cutar, da tantance wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, da wadanda ake zato, da marasa lafiya da ake ganin suna dauke da cutar da wadanda suka yi mu'amula da su, a kuma killace su a wuraren da aka tanada. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China