Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kabilar Hezhe na kokarin samun zaman rayuwa mai wadata
2020-06-26 14:07:19        cri

Iyalin You Mingguo suna rayuwa a kauyen Bacha na kabilar Hezhe dake birnin Tongjiang na lardin Heilongjiang, You Mingguo ya fara aikin kamun kifi tare da mahaifinsa tun lokacin da yake da shekaru 13 da haihuwa.

A karshen karnin da ya gabata, saboda gaza samun kifaye, kabilar Hezhe mai dogaro da aikin su ta fuskanci kalubalen rayuwa. Saboda haka, gwamnatin kasar Sin ta tsai da shirin kebe wa kowane dan kabilar filaye kimanin hekta 4.7 don su fara aikin gona da kiwon dabobbi, hakan ya sa zaman rayuwar jama'ar kabilar Hezhe ya kyautata.

A shekarar 2016, shugaba Xi Jinping ya ziyarci wannan kauye ya gai da jama'ar. A waccan lokaci, You Minguo wanda ke kan matsayin darektan sashen kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen, yana da wani sabon shiri.

Ya karawa mazauna wurin kwarin gwiwar bunkasa sha'anin yawon shakatawa bisa fifiko da kauyen ke da su. A cikin shekaru 3 da suka gabata, yawan masu bude ido da kauyen Bacha ya karba ya wuce dubu 40, kuma yawan kudin shiga da ya samu ya kai fiye da kudin Sin RMB yuan miliyan daya, lamarin da ya kai ga fitar da magidanta 14 dake kunshe da mutane 21 daga kangin talauci.

A cewarsa, yanzu ana da manyan jiragen ruwan shakatawa guda biyu. Kuma yana da shirin hada kai da kasar Rasha don bullo da wata sabuwar hanyar bude ido. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China