Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: An bude tattaunawa game da yaki da fatara
2020-06-23 11:23:18        cri

A jiya Litinin ne kwamitin koli mai aiki karkashin kwamiti na 13, na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ko CPPCC a takaice, ya bude taro na 12 domin tattauna halin da ake ciki, game da yaki da talauci a sassan kasar Sin.

Mataimakin firaministan Sin Hu Chunhua, wanda mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya halarci wannan taro bisa gayyatar da aka yi masa, tare da gabatar da rahoto. Jami'in ya ce, an cimma manyan nasarori a yakin da Sin ke yi da fatara, inda ake gaf da cimma nasarar kammala dukkanin tsare-tsare, da manufofin da aka tsara karkashin shirin.

To sai dai kuma, Hu ya ce Sin na fuskantar mawuyacin yanayi, da kalubale game da kaiwa ga matakin karshe, don haka ya yi kira da a ci gaba da tallafawa matalauta, ta yadda za su ci gaba da aiki, da samarwa marasa ayyuka abun yi, musamman a wannan gaba da ake fama da kalubalen cutar COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China