Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harba tauraron dan Adam na BDS ya jawo hankulan kafofin watsa labarai na kasashen waje
2020-06-24 11:29:55        cri
Kafofin watsa labarai na kasashen waje da dama, sun gabatar da rahotanni game da nasarar da Sin ta samu, ta harba tauraron dan Adam samfurin BeiDou na karshe a ranar Talata, matakin da ya kawo karshen harba taurarin dan Adam dake karkashin wannan rukuni, wadanda kuma ke ba da hidimar taswira.

Tauraron dan Adam din wanda shi ne na 55, cikin rukunin taurarin BeiDou, an harba shi ne da misalin karfe 10 saura mintuna 17 na safiyar ranar Talata bisa agogon birnin Beijing, da rokar Long March-3B, daga tashar harba kumbuna dake Xichang ta lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar.

Nasarar wannan aiki dai na nuni ga ci gaban da Sin ke kara samu a fannin harkokin sama jannati. An kuma bayyana rukunin taurarin na BeiDou, a matsayin daya daga makamantan sa 4 dake aiki a sassan duniya daban daban, wadanda ke samar da hidimar taswira, da tabbatar da lokuta ga sassan duniya.

Sauran makamantan sa 3, sun hada da na GPS dake Amurka, da Galileo na tarayyar turai, da kuma GLONASS na kasar Rasha.

Wani dan sama jannati dake aiki da cibiyar Harvard-Smithsonian ya ce, tsarin ba da hidimar taswira na Beidou-3 muhimmin aiki ne, kuma jari ne mai daraja da Sin ta zuba a wannan fanni, wanda ya ba ta damar tsayawa da kafafunta, maimakon dogaro da Amurka ko tarayyar Turai a fannin samar da wannan hidima. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China