Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce 176,000
2020-06-07 15:46:22        cri

Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Africa CDC ta ce, adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a fadin Afrika a zarce 176,807.

Cikin alkaluma na baya bayan nan da Africa CDC ta fitar ya nuna cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar ya karu daga 171,2016 a maraicen ranar Juma'a zuwa 176,807 ya zuwa yammacin ranar Asabar.

A cewar hukumar, adadin mutanen da annobar ta kashe shi ma ya karu daga 4,766 a yammacin Juma'a zuwa 4,902 ya zuwa yammacin ranar Asabar.

Hukumar dakile cutuka ta nahiyar ta ce, kawo yanzu annobar ta bazu zuwa kasashe 54 na Afrika, kana mutane 78,267 ne suka warke daga cutar ta COVID-19 a fadin nahiyar ya zuwa yanzu.

Africa CDC ta ce, shiyyar arewacin Afrika ne cutar ta fi yi wa illa ta fuskar yawan mutanen da suka kamu da kuma mutanen da cutar ta COVID-19 ta hallaka. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China