Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nace kan aniyarta na yin adawa da nuna wariyar da bambancin launin fata
2020-06-18 10:32:14        cri
Gwamnatin Sin tana goyon bayan Kungiyar Afrika wajen shirya mahawara game da batun yaki da nuna wariya a hukumar kare hakkin dan adam ta MDD, kana kasar Sin ta jaddada aniyarta na yin adawa da duk wani nau'in nuna wariyar launin fata, babban jami'in diflomasiyyar kasar Sin ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, ya yi wannan tsokaci ne a yayin wata mahawara ta gaggawa da aka shirya game da nuna adawa da batun nuna wariyar da take hakkin dan adam da da sauran batutuwa masu alaka da ake fuskanta a halin yanzu. Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ne ta shirya muhawarar bayan bukatar da kasar Burkina Faso ta gabatar a madadin Kungiyar ta Afrika.

Chen ya ce, sun yi matukar kaduwa da bakin ciki bisa mutuwar George Floyd, kana sun mika sakon ta'aziyya ga iyalan jarumin. Rayuwa ita ce sama da komai. Rayuwar bakaken fata tana da muhimmanci.

Ya fadawa MDD cewa a yayin da babban kwamishinan hukumar kare hakkin dan adam na MDD da sauran muhimmai, matakai na musamman sun nuna cewa, mutuwar George Floyd ba shi ne karo na farko ba, ta kuma bankado al'amura da suka jima suna faruwa game da batun nuna wariya, da kisan gillar da 'yan sanda ke aikatawa da kuma nuna rashin daidaito a kasar Amurka.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China