Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: COVID-19 ta haifar da mummunan tasiri ga fannin lafiya, tsaro, da tattalin arzikin Afrika
2020-06-23 10:35:00        cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana cewa annobar COVID-19 da ake fama da ita a halin yanzu ta haifar da mummunan tasiri ga fannin kiwon lafiya, tsaro, da yanayin zamantakewa, da tattalin arzikin nahiyar Afrika.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, AU ta ce, wannan annoba ta COVID-19 da ake fama da ita ta haifar da manyan illoli ga sha'anin kiwon lafiya, tsaro, da tattalin arzikin nahiyar, AU ta jaddada cewa alluran rigakafi su ne kadai mafita da za su taimakawa fannin kiwon lafiyar al'umma, kuma akwai bukatar nahiyar Afrika ta hanzarta shiga aikin samarwa, gwadawa, da amfani da alluran rigakafin annobar ta COVID-19, sannan da batun gwajin alluran rigakafin ga jikin dan adam da sauran batutuwa dake shafar yadda za'a samu damar amfani da su.

Yayin da ake ci gaba da samun yaduwar annobar ta COVID-19 a nahiyar Afrika da sauran sassa na duniya, AU ta jaddada cewa, ingantattun alluran rigakafi za su taimaka wajen ceto rayukan al'umma da tattalin arziki, kuma za su bayar da damar a samu komawar al'amuran yau da kullum sannu a hankali a Afrika da ma duniya baki daya.

Sanarwar AU ta ce, hadin gwiwar nahiyar da yin aiki tare yana da matukar muhimmanci ga aikin samar da allurar rigakafin yaki da annobar ta COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China