Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu cutar COVID-19 a Afirka ya zarta dubu 170
2020-06-06 16:31:55        cri

Alkaluman cibiyar CDC ta Afirka sun nuna cewa, ya zuwa jiya da daddare da misalin karfe 11, jimlar mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Afirka ta kai 171,206, kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai 4,766, kana mutanen da suka warke sun kai 75,083, inda wasu kasashen nahiyar ke ci gaba da saukaka matakan kulle, tare da gabatar da manufofin farfado da tattalin arziki.

Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, ya shaidawa manema labarai a kwanakin baya cewa, rahotanni na nuna cewa, matakan dakile annobar da aka dauka a kasar sun samu sakamako masu gamsarwa, inda ya ce daga ranar 21 ga wata, za a sake bude wasu filayen jiragen saman kasar domin jigila matafiya tsakanin biranen kasar, amma ba a fitar da lokacin dawo da harkokin jiragen saman kasa da kasa ba. Har ila yau, za a sake bude masallatai a fadin kasar, amma ba a sanar da lokacin sake bude makarantun ba tukuna.

Ministan ya kara da cewa, a karkashin hadin gwiwar hukumomin lafiya na kasashen yammacin Afirka, ministocin lafiya na kasashen yankin da yawansu ya kai 15, sun kira taro ta kafar bidiyo, karo na farko tun bayan barkewar annobar, inda suka tattauna kan batutuwan zirga-zirgar mutane tsakanin kasa da kasa da sayen kayayyakin kiwon lafiya daga kasar Sin da sauransu.

Hakazalika, kasashen duniya za su ci gaba da samar da tallafi ga kasashen Afirka wajen dakile annobar, inda a jiya Juma'a, gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, ta samu wasu kayayyakin kiwon lafiya daga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China