Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce 180,000
2020-06-08 14:36:00        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC, ta ce jimillar mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya kai 183,474.

Cikin alkaluman baya bayan nan da Africa CDC ta fitar ya nuna cewa, adadin mutanen da suka kamu da annobar ta COVID-19 ya karu daga 176,807 a yammacin ranar Asabar zuwa 183,474 a yammacin ranar Lahadi.

Adadin mutanen da cutar ta hallaka shi ma ya karu daga 4,902 a yammacin ranar Asabar zuwa 5,041 a yammacin ranar Lahadi, a cewar hukumar ta Africa CDC.

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta nahiyar ta ce, kawo yanzu, cutar ta yadu zuwa kasashen Afrika 54, kana an samu adadin mutanen da suka warke daga cutar ta COVID-19 a fadin nahiyar Afrika kimanin 81,367 ya zuwa yanzu.

Afrika CDC ta ce shiyyar arewacin Afrika ne cutar ta fi yiwa illa ta fuskar adadin mutanen da suka kamu da kuma wadanda annobar ta COVID-19 ta kashe.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China