Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun kasar Sin sun mika shawara ga Guinea Bissau a fannin yakar COVID-19
2020-06-07 20:09:22        cri

A ranar 5 ga wata, bisa gayyatar da firaministan kasar Guinea Bissau, Francisco Obama Asue ya yi, wata tawagar kwararrun masana ilimin aikin likitanci ta kasar Sin ta ziyarci babban yankin kasar, inda masanan suka yi musayar ra'ayi tare da karamin minista mai kula da aikin kiwon lafiya da moriyar jama'a na kasar Nguema.

Mista Nguema ya nuna yabo kan ayyukan da tawagar masanan kasar Sin suke gudanarwa a kasarsa, gami da nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin. A nasa bangare, Zhu Yimin, shugaban tawagar masanan Sin, ya mika takardar bayani ga mista Nguema, game da shawarar da aka baiwa kasar Guinea-Bissau a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19. A cewarsa, kwararrun kasar Sin sun gabatar da shawarwarin ne bisa bayanan da suka samu dangane da ainihin yanayin da kasar Guinea-Bissau ke ciki a fannin yaki da cutar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China