Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutane masu cutar COVID-19 a Afirka ya zarta dubu 280
2020-06-21 17:14:10        cri

Alkaluman da cibiyar CDC ta Afirka ta fitar a jiya ranar 20 ga wata sun nuna cewa, gaba daya adadin mutanen kasashen nahiyar Afirka wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai 287385, a ciki, adadin masu cutar da suka rasa rayuka ya kai 7708, kana adadin masu cutar da suka warke ya kai 132959.

Hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD ta bayyana jiya Asabar cewa, hukumar da CDC ta Afirka za su samar da dandalin musayar bayanai kan cutar cikin hadin gwiwa, domin kandagarkin yaduwar cutar yadda ya kamata.

Hukumar ta kara da cewa, za a samar da dandalin ne ta hanyar yin amfani da manhajar wayar salula, wanda zai gabatar da sabbin shawarwari game da kiwon lafiyar jama'a da ci gaban tattalin arziki ga masu amfani da manhajar wadanda suka kai sama da miliyan 600 a nahiyar, tare kuma da samar da hidima ga tawagogin likitocin kandagarkin annobar a kasashen da shiyyoyin nahiyar.

A ranar 19 ga wata ma'aikatar kiwon lafiyar Nijar ta bayyana cewa, kasar za ta daina samar da takardun iznin tafiya na musamman ga masu tafiya a iyakar kasa, sakamakon dalilin karuwar masu cutar da suka shiga kasar daga ketare da tsananin yanayin kandagarkin annobar COVID-19 da kasar ke ciki.

Kana bankin duniya ya sanar a jiya cewa, zai samar da tallafin kudi da rancen kudi da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 100 ga Senegal domin taimaka mata a bangaren rage tasirin illar da annobar COVID-19 ta haifar, tare kuma da samar da taimako ga masu cutar wadanda ke fama da talauci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China