2020-06-23 10:16:19 cri |
Kudurin mai lakabin "Bunkasa hadin gwiwar cin moriyar juna a fannin kare hakkokin bil Adama," ya jaddada muhimmancin habaka cudanyar kasa da kasa bisa martaba juna, da daidaito, da adalci, da cin gajiya tare. Kana da gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin al'ummar duniya, wadda kowane mutum zai iya amfana da kariyarta ta fannin hakkin dan Adam.
Har ila yau, kudurin ya yi kira ga dukkanin kasashe, da sassa masu ruwa da tsaki, da su shiga a dama da su, yayin tattaunawa mai ma'ana, da cudanya, da hadin gwiwa a fannin kare hakkin bil Adama, karkashin tsarin habaka, da rashin nuna banbanci, da hangen nesa, da kaucewa rabuwar kawuna, da bangaranci, da kaucewa shigar da siyasa.
Bugu da kari kudurin na fatan dukkanin sassan za su rungumi akidun tabbatar da daidaito, da girmama juna, domin bunkasa cikakkiyar fahimtar juna, da fadada ginshikin manufar tafiya tare, da rage bambance-bambance, da karfafa hadin gwiwa mai ma'ana. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China