Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya yabawa gudunmuwar kasar Sin wajen yaki da COVID-19 a duniya
2020-02-25 11:39:57        cri

Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya yabawa gudunmuwar da kasar Sin ta bayar a yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, yana mai cewa Sinawa na kokarin kare bani adam.

Bayan ya tattauna kan barkewar cutar COVID-19 da Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, jiya a Geneva, Antonio Guterres ya yi kira ga dukkan kasashen duniya su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na yaki da cutar.

Sakatare Janar din ya bukaci dukkan kasashen duniya, su yi iyakar kokarin zama cikin shirin yakar annobar, yana mai jaddada cewa, ya kamata a girmama ka'idar rashin nuna bambanci da kyama da kuma kare hakkin dan Adam yayin yaki da cutar.

A amsar da ya bayar dangane da tambayar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi masa, Guterres ya godewa dukkan al'ummar kasar Sin da suka sadaukar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum domin hana yaduwar cutar.

Ya ce raguwar yawan sabbin masu kamuwa da cutar tun daga farkon watan Fabrairu, alama ce mai kyau, inda ya yi fatan za a ci gaba da samun raguwar adadin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China