2019-08-14 13:12:40 cri |
Zhang Jun wanda ya bayyana hakan yayin taron kwamitin sulhun MDD game da yayata ta karfafa doka yayin tabbatar da ayyukan zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, ya ce, yarjeniyoyin da aka cimma a Geneva da ragowar yarjeniyoyi, sun kasance muhimman ka'idojin da suka shafi bil-Adam wadanda suka samu goyon bayan dukkan kasashen duniya.
Ya ce, a halin yanzu, yanayin tsaron duniya ya kasance mai hadari gami da sabbin abubuwan ban tsaro da ke sake kunno kai. An kara samun yaduwar tashin hankali na masu dauke da makamai a wasu shiyyoyin, lamarin da ya haifar da mummunar damuwa ga al'ummomin duniya.
Jami'in na kasar Sin ya ce, ya kamata a kowane yanayi, gwamnatoci su sauke nauyin dake bisa wuyansu ta hanyar martaba dokar jin kai ta kasa da kasa, kuma wannan tsari ba zai sauya ba. Yana mai cewa, idan har ba za a iya kaucewa tashin hankali ba, to, ya kamata a martaba ka'idojin dokar jin kai ta kasa da kasa, don hana amfani da karfi ba gaira ba dalili ko wasu ayyukan da za su yi mummunan tasiri ga harkokin jin kai.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China