Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira da a kawar da abubuwan dake haifar da rikice-rikice masu dauke da makamai tun daga tushe
2019-06-12 09:36:26        cri

Zaunannen Jakadan kasar Sin a MDD, Ma Zhaoxu, ya yi kira ga kasa da kasa, da su kawar da abubuwan dake haifar da rikice-rikice masu dauke da makamai tun daga tushe, domin kawo karshen batar mutane yayin irin rikicin.

Ma Zhaoxu, ya shaida wa taron kwamitin sulhu na MDD kan kare fararen hula da batar mutane yayin rikice-rikice masu dauke da makamai cewa, kamata ya yi kwamitin sulhu ya jajjirce wajen sauke hakikanin hakkin da aka rataya a wuyansa, na tabbatar da tsaro da zaman lafiya da inganta warware sabani bisa tattaunawa da tuntuba da yarjeniyoyin siyasa domin hana aukuwar rikici da warware takkadama cikin ruwan sanyi da kuma rage rikice-rikice masu dauke da makamai.

Jakadan ya kara da cewa, dole ne a yi adawa da tsoffin akidu kamar rikici tsakanin al'adu iri daban daban da yakin cacar baka da cin moriya da faduwar wani, domin kulla abota mai aminci da kauracewa fito-na-fito da kuma aiki tare don samar da misali ga sabon nau'in dangantakar kasa da kasa bisa adalci da mutunta juna da daidaito da kuma cin moriyar juna, a wani kokari na hadin gwiwa don gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China