Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar zaunannun wakilan Sin dake MDD ta yi liyafar murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2019-09-21 16:42:02        cri

Tawagar zaunannun wakilan Sin dake MDD ta yi liyafar murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin a jiya da daddare.

A gun liyafar, jakadan Sin Zhang Jun ya bayyana cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, an kirkiro hanyar raya kasar Sin karkashin tsarin gurguzu na musamman bisa yanayin da ake ciki a kasar, da hada makomar kasar Sin da makomar duniya, da samar da shirye-shiryen don samar da gudummawar raya duniya, da kuma samar da sabbin damarmaki.

Zhang Jun ya yi nuni da cewa, a matsayin daya daga cikin membobin farko da suka kafa MDD, Sin da MDD sun yi kokari tare, da zama abokan hadin gwiwa. Ya ce Sin ta tabbatar da ra'ayin bangarori daban daban, da shimfida zaman lafiya a duniya, da samar da gudummawa wajen raya duniya, da kuma nuna goyon baya ga MDD. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da cika alkawarin da ta yi wa MDD da sha'anin kiyaye ra'ayin bangarori daban daban, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da MDD da membobinta, da sa kaimi ga kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da kuma raya kasar Sin da ma duniya zuwa wani sabon mataki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China