Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dr. Austin Maho: Kasar Sin na jagorantar duniya dakile COVID-19
2020-06-20 17:19:08        cri

Kwanan nan, babban editan jaridar Daybreak ta tarayyar Najeriya, Dr. Austin Maho ya wallafa wani sharhi mai taken "Shugaba Xi Jinping ya sake jaddada zumunci dake tsakanin Sin da Afirka, samar da allurar rigakafi da soke basussuka sun zama muhimman jadawali". A cewarsa, an samu babbar nasara a wajen taron koli na musamman na hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen dakile yaduwar COVID-19, kuma bangarorin biyu sun cimma matsaya da fitar da sanarwa cikin hadin-gwiwa, da karfafa dadadden zumuncinsu da kara samun fahimtar juna a tsakaninsu, al'amarin da ya nuna irin jagoranci mai karfi na kasar Sin a sha'anin dakile annobar a duk fadin duniya baki daya.

Sharhin ya ce, kasar Sin ta yi alkawarin cewa, idan ta kammala aikin bincike gami da fara amfani da allurar rigakafin cutar COVID-19, nahiyar Afirka ce za ta fara amfana. Hakan na shaida ainihin zumunci da hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Har wa yau, sharhin ya ce, akwai kasashen Afirka da dama wadanda ke fuskantar babbar matsalar tawayar tattalin arziki sakamakon bazuwar cutar COVID-19, kuma irin abun da kasar Sin ta yi, wato soke basussukan da take bin Afirka, ya taimaka sosai ga kasashe marasa ci gaba a nahiyar, da nuna aniyar kasar Sin na goyon-bayan kasashen Afirka samun ci gaba mai dorewa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China