Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa game da karuwar masu kamuwa da COVD-19 a kasar
2020-06-12 19:19:34        cri
Mahukuntan Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda aka samu sabbin wadanda suka kamu da COVID-19 da ya kai sama da 600 sau biyu a wannan mako.

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, kana Shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 da shugaban kasar ya kafa, Boss Mustapha shi ne ya bayyana haka jiya Alhamis, yayin taron manema labaru a Abuja, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, lamarin abin damuwa ne,

Mustapha ya ce, da dama daga 'yan kasar ba sa kare kansu daga cutar, inda ya yi gargadin cewa, idan har mutane suka bari cutar ta kara yaduwa tsakanin jama'a, to hakan na iya zama babban hadari. Don haka ya jaddada bukatar sanya ido da kare kai.

Ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan yadda jama'a ke martaba dokokin da aka sanya a kasa baki daya, za kuma ta ci gaba da tuntubar bangarorin da suka dace.

Yanzu haka yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar ya haura 14,000. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China