Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu ranar bude makarantu a Najeriya
2020-06-09 20:42:16        cri
Karamin minista a ma'aikatar Ilimi ta Najeriya Emeka Nwajiuba, ya sanar a jiya Litinin cewa, har yanzu ba a sanya ranar bude makarantu a sassan kasar ba.

Ministan ya shaidawa taron manema labarai na rana-rana da ma'aikatar ke shiryawa game da yanayin cutar COVID-19 cewa, jita-jitar da ake ta yayatawa cewa, za a bude makarantu a ranar 21 ga watan Yuni ba gaskiya ba ne, kuma ba ma'aikatar ce ta fada ba.

A cewarsa, ma'aikatar Ilimin kasar, ba za ta yi gaggawar bude makarantun da ka iya jefa 'yan kasar cikin hadari ba. Yana mai cewa, za a bude makarantun ne kawai idan har aka tabbatar cewa, babu wani hadari a yin haka. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China