Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsaloli da dana sun dakatar da sake bude filayen jiragen saman Najeriya
2020-06-19 10:25:18        cri
Shirin Najeriya na sake bude filayen jiragen sama na cikin gida, tun daga ranar 21 ga watan nan ya gamu da cikas, bayan da masu ruwa da tsaki a fannin suka ce akwai tarin kalubale, masu nasaba da bazuwar cutar COVID-19, da ka iya dakatar da wannan aniya.

Bayan wata tattaunawa tsakanin majalissar dattawan kasar da wakilan ma'aikatan sufurin saman kasar a jiya Alhamis, majalissar ta dattawa ta ce, ba zai yiwu a iya sake bude zirga-zirgar fasinja ta sama ba.

A nasu bangaren, wakilan ma'aikatan sufurin jiragen saman kasar, sun ce akwai bukatar samar da kudaden tallafi na musamman, da managarcin tsarin gudanarwa, da na kariya, duba da halin da ake ciki na yaki da bazuwar cutar COVID-19, kafin a kai ga sake bude filayen jiragen saman.

A wani ci gaban kuma, hukumar sufurin jiragen saman kasar NCAA, ta ce ba za a iya bude filayen jiragen saman kasar kamar yadda aka tsara a baya ba. A cewar babban daraktan hukumar Musa Nuhu, NCAA ba za ta amince da sake bude zirga-zirgar jiragen sama ba, har sai ta gamsu cewa, za a iya gudanar da sufurin fasinjoji cikin tsari, da kuma tsaron lafiyar kowa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China