Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hasashe: Miliyoyin 'yan Najeriya na iya rasa ayyukan yi sakamakon COVID-19
2020-06-12 10:17:53        cri
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya ce kusan 'yan Najeriya miliyan 40 ne ka iya rasa guraban su na ayyukan yi, zuwa karshen wannan shekara ta 2020, sakamakon aiwatar da matakan dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Yemi Osinbajo, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, lokacin da yake hakaito alkaluman da hukumar kididdigar kasar NBS ta fitar game da hakan. To sai dai kuma ya ce, ana iya daukar wasu matakai na shawo kan wannan kalubale.

Ya ce alkaluman na NBS sun nuna cewa, akwai yiwuwar 'yan Najeriya miliyan 39.4, kwatankwacin kaso 33.6 bisa dari na daukacin al'ummar kasar za su tsunduma cikin matsalar rashin ayyukan yi.

Sakamakon wani bincike da hukumar NBS ta gudanar bisa umarnin kwamitin wanzar da managarcin yanayin tattalin arziki a Najeriyar, kwamitin da Mr. Osinbajo ke jagoranta, ya nuna cewa, karin 'yan kasar da dama na fuskantar hatsarin fadawa yanayi na tsananin talauci, kafin a kai ga shawo kan cutar baki daya.

Da yake karin haske game da hakan, yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin ga shugaban kasar Muhammadu Buhari, Mr. Osinbajo ya ce matakan da ake aiwatarwa na dakile yaduwar COVID-19, sun riga sun fara haifar da mummunan tasiri kan manoma da masana'antu, da ma harkokin cinikayya, da sufuri da kuma fannin yawon bude ido.

Don haka a cewar sa, idan ana son kirkirar miliyoyin sabbin guraben ayyukan yi, ya zama dole a karfafa gwiwar sassan sarrafa hajoji, da fannin kirkire-kirkire a cikin cikin gida, tare da ba da muhimmanci ga bunkasa kasuwancin gida. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China