Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHCR na neman mafita dangane da batun 'yan gudun hijira a yankin gabashin Afrika yayin da ake fama da COVID-19
2020-05-27 09:30:30        cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR, ta ce tana aiki da abokan hulda da gwamnatoci a yankin gabashin Afrika, domin samo mafita dangane da 'yan gudun hijirar dake birane a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen COVID-19.

Wata sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce, 'yan gudun hijirar dake birane na fafutukar rayuwa da neman muhimman bukatunsu, yayin da tasirin COVID-19 kan tattalin arziki ke kara muni a yankunan gabashi da kahon Afrika da kuma manyan tafkunan nahiyar.

Hukumar na neman shilling biliyan 13.4, kwatankwacin dala miliyan 126, domin ayyukan ceton rai na yaki da COVID-19 a wadancan yankunan.

Sai dai, hukumar na fargabar idan ba a samu tallafi ba, galibin 'yan gudun hijirar za su fada cikin yanayin matsi da hadarin fadawa kangin bashi da ka iya tilasta musu shiga matsanancin yanayi domin rayuwa, kamar karuwanci da bautar da yara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China