Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika sun daidaita matakan kandagarkin COVID 19, Sin tana ci gaba da taimaka musu
2020-05-21 12:56:28        cri

Bisa halin da ake ciki, kasashen Afrika da dama sun daidaita matakan kandagarkin COVID 19, kasar Sin kuma za ta ci gaba da taimaka musu a wannan fanni.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya yi afuwa ga fursunoni 400 a daren ranar 19 ga wata, don hana yaduwar cutar a gidajen kurkuku.

Ma'aikatar tattalin arziki da kudi ta Cote D'ivoire ta nuna a jiya 20 ga wata cewa, kasar ta zuba kudi Franc na yammacin Afrika biliyan 3.382 don tallafawa kamfanoni da daidaikun mutane da cutar ta rutsa da su.

Ban da wannan kuma, kasar Senegal ta samar da rancen kudi a ranar 19 ga wata na kudin Franc na yammacin Afrika biliyan 3.7 don sa kaimi ga sha'anin otel da yawon shakatawa a kasar.

Dadin dadawa, AU ta tura masana kiwon lafiyar Kongo Kinshasa 38 da cibiyar CDC ta Afirka ta zaba zuwa kasashen Kamaru da Nijer da Burkina Faso da Mali a ranar 19 ga wata domin taimake su a bangaren kandagarkin annobar.

Haka zalika, masanan kasar Sin sun kai ziyara a wurare dabam-daban a Zimbabwe daga ranar 18 zuwa 20, da kuma rarraba fasahohi da dabarunsu ga jami'an kiwon lafiya da masu jiyya a wurin a fannin tsarin kandagarki da bin diddigin wadanda suka yi mu'ammala da mutanen da cutar ta harba, da ba da jiyya ga masu cutar da killacewa da dai sauransu. Ban da wannan kuma, tawagar masanan ta samarwa hukumomin jiyya kayayyakin aikin jiyya.

Ban da wannan kuma, ofishin jakadancin Sin dake Mauritaniya ya baiwa ma'aikatar samar da guraben aikin yi da ta matasa da motsa jiki wasu na'urorin dinka riguna don samar da marufin baki da hanci da dai sauran abubuwan kandagarki, tare kuma da samar da guraben aikin yi a wurin ga matasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China