Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 70 yayin wani samame
2020-06-07 15:47:54        cri
A kalla 'yan bindiga 70 aka kashe yayin ayyukan sintiri da sojojin Najeriya suka kaddamar a jihar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

John Enenche, kakakin sojojin Najeriyar ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce 'yan bindigar wadanda hukumomi sun yi amanna cewa 'yan fashi ne da barayin shanu, an hallaka su a dajin Kashia, daya daga cikin wuraren da barayin ke amfani da shi a matsayin mafakarsu dake jihar.

Shirin sintirin sojojin yana daya daga cikin muhimman ayyukan da sojoji suka bullo da shi a shiyyar arewaci maso yammacin kasar bayan da yankin ya shafe shekaru yana fama da ayyukan bata gari.

Enenche ya ce, sojojin suna cigaba da farautar barayin tun daga yankunan karamar hukumar Chikun zuwa cikin dajin, kana sun sha kaddamar da hare-hare kan 'yan bindigar ta jiragen helikwafta domin tarwatsa maboyarsu. Da dama daga cikin barayin sun tsere da raunuka kuma sojojin za su cigaba da kaddamar da farmaki kan barayin a cikin dajin.

Ayyukan 'yan bindiga, da masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da sauran ayyukan bata gari, suna cigaba da ta'azara a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Sai dai rundunar sojojin kasar ta sha nanata aniyarta na dakile ayyukan bata garin da murkushe 'yan bindigar da suka addabi yankin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China