Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen yakar COVID-19 zai amfani duniya
2020-06-18 20:01:30        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Alhamis cewa, jiya ne aka yi nasarar gudanar da taron kolin musamman na kasashen Sin da Afirka kan yaki da annobar COVID-19, kuma, kara inganta alaka da hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar yakar annobar, zai farfado da imanin duniya, tare da kafa sabon misali ga kasa da kasa.

A yayin taron kolin, kasar Sin ta ce za ta kara daukar matakan tallafawa kasashen Afirka dakile annobar, da rage musu basussuka, da taimaka musu wajen daidaita matsalolin tattalin arzikin da suke fuskanta. Amma akwai wasu kafafen yada labarai wadanda ke ganin cewa, makasudin shirya irin wannan taro shi ne, domin kasar Sin na son fadada tasirinta a nahiyar ta Afirka.

Game da wannan batu, Zhao Lijian ya ce, shugabannin kasashen Afirka da dama suna ganin cewa, taron kolin ya karfafa imaninsu wajen kawar da wannan cuta, kuma kasar Sin tana baiwa kasashen Afirka taimako a daidai lokacin da suke bukata. Sin da Afirka aminan juna ne na kwarai. Zhao ya kara da cewa, cutar COVID-19 na ci gaba da bazuwa a Afirka, abun da ya sa kasashen nahiyar ke kara fuskantar kalubale. A don haka, kasar Sin ta yi kira ga kasa da kasa su saurari muryoyin kasashen Afirka, da maida martani kan bukatunsu, tare kuma da kara ba su taimako a fannin dakile annobar da neman ci gaba mai dorewa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China