![]() |
|
2020-06-07 16:38:33 cri |
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labaru a Lahadi don gabatar da wata takardar bayani dangane da matakan da kasar Sin ta dauka a kokarin dakile cutar COVID -19. Inda Wang Zhigang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin, ya jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin bangarorin kasa da kasa, a yunkurin samar da allurar rigakafin cutar.
A cewarsa, wannan hadin gwiwa zai shafi aikin nazari, gami da gwaje-gwajen amfani da allurar. Sa'an nan bayan da aka gama nazarin allurar, kasar Sin za ta samar da rigakafin kyauta ga kasashe daban daban, a matsayin wani magani na jama'a. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China