![]() |
|
2020-06-04 20:30:48 cri |
A yau Alhamis kwamitin tsakiya na JKS, ya kira taron kungiyar ba da jagoranci kan aikin dakile cutar COVID-19, a yayin taron aka yi nuni da cewa, yanzu haka an samu sabuwar nasara a fannin nazarin allurar rigakafin wannan cuta a kasar Sin, nan gaba kuma za a ci gaba da yin gwaji a jikin mutane, domin samar da allurar ba tare da jinkiri ba.
Kaza lika an nuna cewa, yanayin dakile annobar da kasar Sin ke ciki yana da kyau, amma duk da haka, kasar tana fama da hadarin shigar cutar daga ketare, don haka za a kara karfafa wannan aiki, ta yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar cikin lumana. (Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China