Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Gabatar Da Takardar Bayani Dangane Da Matakan Da Kasar Sin Ta Dauka Na Yaki Da COVID-19
2020-06-07 16:42:07        cri

A yau Lahadi, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani dangane da matakan da kasar ta dauka na yaki da cutar COVID-19.

Cikin wannan takarda, an yi cikakken bayani kan wahalhalun da kasar Sin ta haye, da matakan da ta dauka, don dakile yaduwar cutar COVID-19, da jinyar masu kamuwa da cutar, da kokarin hadin gwiwa da bangarori daban daban, gami da kokarin kafa wata al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya a fannin kiwon lafiya.

An bayyana a cikin wannan takardar bayani cewa, bayan barkewar cutar COVID-19 a kasar Sin, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mista Xi Jinping, ya jagoranci aikin dakile cutar shi da kansa, inda ya jaddada bukatar mai da rayuka da lafiyar jikin jama'a a gaban kome.

Sa'an nan an ambaci yadda kasar Sin ta dauki kwararrun matakai, wadanda suka shafi dukkan bangarorin kasar, don tabbatar da ganin an kula da duk wanda ya kamu da cutar, da kokarin kare lafiyar jikin jama'a ba tare da tsimin kudi ko albarkatu ba.

An kuma bayyana yadda kasar Sin ta samu hana yaduwar cutar cikin gajeren lokaci, da kokarin hadin gwiwa da bangarorin kasa da kasa, da raba fasahohinta a fannin yakar cutar ba tare da rufa-rufa ba, duk domin neman kafa wata al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya a fannin kiwon lafiya, da ganin bayan annobar cikin sauri. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China