Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan samar da rigakafin cutar COVID-19
2020-06-05 19:58:23        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce, Sin za ta yi aiki tukuru, wajen zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa, kan gudanar da bincike, da samar da rigakafin cutar numfashi ta COVID-19.

Jami'in ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan kafuwar al'umma mai makoma guda ga daukacin bil Adama, za ta kuma yi aiki kafada da kafada, da dukkanin sassan masu ruwa da tsaki, wajen binciken rigakafi, da hadin gwiwar kasa da kasa, har sai an kai ga dakile wannan annoba cikin hanzari.

Kan taron kasa da kasa game da rigakafi da aka gudanar ta kafar bidiyo, Geng ya ce Sin ta gamsu, da yadda dukkanin sassa da suka shiga wannan taro, suka sha alwashin karfafa hadin gwiwa, wajen ci gaba da binciken rigakafin, da samar da shi, yana mai jaddada karfin gwiwa da jajircewar kasa da kasa wajen hada hannu, a fannin yaki da wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China