Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Beijing: Za a kara sassauta matakan yaki da COVID-19 zuwa matsayi na uku
2020-06-05 20:23:54        cri

Mahukuntan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, sun ce za a sassauta matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19, zuwa matsayi na uku, tun daga ranar Asabar 6 ga watan nan na Yuni.

A cewar Chen Bei, mataimakiyar babban sakataren gwamnatin birnin, yayin wani taron manema labarai a Juma'ar nan, za a ci gaba da daidaita matakan kandagarki, da na shawo kan cutar ta COVID-19 gwargwadon sauyin yanayi da ake samu.

A cewar jami'ar, za a janye tarnakin da aka sanya kan sayen tikitin jiragen sama, da na kasa, ga matafiya masu fitowa daga lardin Hubei zuwa birnin Beijing, ciki hadda matafi daga birnin Wuhan, inda cutar ta fara bulla. Hakan dai na nufin al'ummun da suka fito daga Wuhan, ba sai an killace su tsawon kwanaki 14 ba, kana ba bu bukatar ci gaba da sanya idanu a kan su, bayan sun iso birnin Beijing.

Bugu da kari, ba bu bukatar gwada zafin jikin mazauna unguwanni, duk da cewa za a ci gaba da yin rijistar masu shiga da fita daga unguwannin.

A daya hannun kuma, kamfanoni dake samar da kayan bukata na wajibi, da wadanda ke samar da muhimman hidimomi, za su iya komawa bakin aiki karkashin cikakken tsarin kulawa, da sanya ido don tabbatar da dakile sake bullar cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China