Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A Beijing an samu rahoton sabbin mutane 21 da suka kamu da COVID-19
2020-06-18 10:44:15        cri

Hukumar kiwon lafiyar birnin Beijing ta bada rahoton sabbin mutane 21 da suka kamu da annobar COVID-19 da wasu sabbi uku wadanda ba sa nuna alamomin kamuwa da cutar a ranar Laraba.

Ya zuwa ranar Laraba, Beijing ta bada rahoton jimillar mutane 578 sun kamu da cutar a cikin gida, daga ciki akwai mutane 411 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar da kuma mutane 9 da suka mutu. Har yanzu akwai mutane 158 da ake kula da lafiyarsu a asibiti, da wasu mutanen 15 da ba su nuna alamomin kamuwa da cutar inda ake kula da su a asibiti.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China