Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin mutane 6 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Beijing
2020-06-13 15:24:34        cri
Hukumomi a birnin Beijing na kasar Sin, sun bada rahoton samun sabbin mutane 6 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a jiya Juma'a.

Yayin wani taron manema labarai na cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Beijing da aka yi da safiyar yau Asabar, an bayyana cewa, baya ga ma'aikatan cibiyar binciken abinci da nama ta kasar Sin dake gundumar Fengtai ta birnin Beijing da aka tabbatar sun kamu da cutar da sanyin safiyar jiya Juma'a, tsakanin karfe 4 na yamma zuwa 12 na dare a jiyan, an kuma samu rahoton wasu mutane 4 da suka kamu.

Kuma dukkan mutanen 4, sun ziyarci kasuwar sayar da amfanin gona ta Xinfadi dake gundumar Fengtai.

A cewar mataimakiyar shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtukan, Pang Xinghuo, binciken farko-farko ya nuna cewa, akwai yuwuwar mutanen sun yi cudanya da wasu masu cutar a kasuwar, ko kuma sun je wani gurbataccen wuri. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China