Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An daga matsayin fuskantar harkar kiwon lafiya ta gaggawa daga matsayi na uku zuwa matsayi na biyu a birnin Beijing
2020-06-17 13:55:03        cri

Daga ranar 16 ga wata, an daga matsayin fuskantar harkar kiwon lafiya ta gaggawa, daga matsayi na uku zuwa matsayi na biyu a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Bayan shafe kwanaki 57 ba tare da samun sabbin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Beijing ba, a ranar 11 ga watan Yuni, an sake gano wasu masu dauke da cutar a birnin Beijing.

Ya zuwa ranar 15 ga wata, gaba daya, an tabbatar da mutane 116 da suka harbu da cutar, ciki har da mutane 10 da ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba. Kana, dukkansu suna da alaka da kasuwar Xinfadi dake kudancin birnin Beijing.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China