Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwajin makogwaro na cutar COVID-19 da aka yi a Beijing ya tabbatar da mutane 46 sun dauki kwayar cutar
2020-06-13 15:57:55        cri
Jimilar mutane 46 ne aka tabbatar sun dauki kwayar cutar COVID-19, bayan gwajin da hukumomi suka gudanar a manyan kasuwannin sarin amfanin gona da manyan shagunan sayar da kayayyaki dake birnin Beijing na kasar Sin.

Yayin taron manema labarai da aka yi da safiyar yau, mataimakiyar shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta birnin Beijing, Pang Xinhghuo, ta ce jami'an cibiyar, sun gudanar da gwaji kan mutane 1,940 a kasuwannin. Kuma daga cikin samfura 517 da aka karbo daga babbar kasuwar sarin kayayyaki ta Xinfadi, an tabbatar da 45 na daukar kwayar cutar.

An kuma samu wanda ke dauke da kwayar cutar daga gwajin da aka yi a kasuwar sayar da amfanin gona ta gundumar Haidian na birnin, wanda ake ganin ya harbu ne sanaddiyar cudanya da mai cutar a kasuwar Xinfadi.

Dukkan mutanen 46 ba su nuna alamun dauke da kwayar cutar ba, amma ana nazartarsu tare da sa musu ido yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China