2020-06-14 17:14:11 cri |
A ranar Asabar an tabbatar da samun sabbin mutane 36 wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wani mutum guda da ke dauke da cutar wanda bai nuna alamomin cutar ba, kamar yadda hukumar lafiyar gwamnatin birnin Beijing ta tabbatar da hakan.
Pang Xinghuo, mataimakiyar daraktan cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Beijing, ta fadawa taron manema labarai cewa an bi diddigin dukkan wadanda suka kamu da cutar kuma an gano suna da alaka da kasuwar Xinfadi dake kudancin birnin Beijing.
Pang ta yi cikakken bayani game da kowane mutum guda cikin adadin wadanda suka kamu da cutar, inda aka gano ko dai marasa lafiyar sun yi aiki a kasuwar ko kuma sun yi mu'amalar kai tsaye da wacce ba ta kai tsaye ba da wannan kasuwa.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China