Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
2020: Cinikayyar waje ta Sin na fuskantar babban kalubale
2020-06-17 12:32:16        cri

Fannin hada hadar cinikayyar waje ta Sin, na fuskantar babban kalubale a bana, sakamakon rashin tabbas da cutar COVID-19 ta haifar a fannin kasuwancin kasa da kasa.

Wani rahoto da ma'aikatar cinikayya ta Sin ta fitar ne ya bayyana hakan. Rahoton ya ce hadarin fadawar kasashen duniya cikin yanayi na matsin tattalin arziki na karuwa, kana yanayin bukatun hajojin da masana'antu ke sarrafawa ya gamu da tangarda, wanda hakan ya haifar da raguwar hada hadar cinikayyar waje da harkokin zuba jari.

A hannu guda kuma, rahoton ya bayyana yadda kamfanonin cikin kasar ta Sin, musamman ma kanana da matsakaita ke fuskantar karin matsaloli da matsi ta fuskar kwadago.

To sai dai kuma a gabar da harkokin tattalin arzikin kasar ke kara daidaita, akwai kakkarfan ginshiki dake saita ci gaban daukacin sassan hada-hadar cinikayya, da zuba jarin waje na kasar Sin.

Rahoton ya kara da cewa, karkashin bukatar daidaita cinikayyar hajoji a matakin kasa da kasa, da bukatar ci gaba da aiwatar da hada-hadar hajojin masana'antu, an kaddamar da baje kolin Canton na bana, wanda shi ne karo na 127, a jerin baje kolin hajojin da ake shigowa da su da wadanda ake fitarwa daga kasar Sin.

An bude baje koli na bana ne a ranar Litinin ta kafar bidiyo, a birnin Gunagzhou, fadar mulkin lardin Guangdong. Baje kolin na bana wanda za a shafe kwanaki 10 ana gudanarwa, ya samu halartar kamfanoni 25,000, da kuma dubun dubatar masu sayayya, inda kuma aka baje hajojin da yawansu ya kai miliyan 1.8. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China