![]() |
|
2019-09-13 20:13:51 cri |
A wani ci gaban kuma, mahukuntan kasar ta Sin sun nuna goyon baya ga wasu kamfanonin Sin, wadanda ke fatan sayo wasu albarkatun gona daga Amurka, bisa tanajin kasuwanni, da kuma tsarin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kamar dai yadda wata majiya daga hukumar tsara ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar, da ma'aikatar cinikayyar kasar suka bayyana.
Wannan mataki dai na zuwa ne, bayan da Amurka ta yanke shawarar yin wasu sauye sauye, game da harajin da ta ayyana karawa kan hajojin Sin dake shiga kasar, tun daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China