Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na hangen babbar nasara a fannin hadin gwiwar ta da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya
2020-05-15 11:22:20        cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce akwai nasara mai tarin yawa a fannin hadin gwiwar Sin da sauran kasashen da suka rungumi shawarar ziri daya da hanya daya.

Da yake karin haske game da hakan, yayin wani taron manema labarai, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce duk da cewa COVID-19 ta yi tasiri ga tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, a hannu guda, akwai managarcin ginshiki, da babbar dama ta bunkasa hadin gwiwar sassan ta fannin ci gaba.

Wasu alkaluma da ma'aikatar cinikayyar ta fitar sun nuna cewa, darajar hada hadar cinikayya tsakanin Sin da kasashen da suka shiga wannan shawara, wadda ta kai kaso 30.4 bisa dari, na jimillar hada hadar ta da sauran sassan duniya ta daga da kaso 0.9 bisa dari a shekara guda, inda a a watanni 4 na farkon shekarar, adadin ya daga zuwa yuan tiriliyan 2.76, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 388.73.

Adadin dai ya haura kaso 4.9 bisa dari na faduwar da kasar ta samu, a fannin hada hadar cinikayyar waje a shekara guda.

Gao ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasashen da suka shiga wannan shawara ta ziri daya da hanya daya, wajen yaki da cutar COVID-19, za ta kuma karfafa tsarin hadin gwiwar habaka tattalin arziki da cinikayya da wadannan kasashe. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China