Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji sun halaka 'yan bindiga sama da 300 a Najeriya
2020-06-05 10:06:06        cri

Babban hafsan mayakan sama na Najeriya Sadiq Abubakar, ya tabbatar jiya Alhamis cewa, dakarun saman kasar sun yi nasarar kashe sama da 'yan bindiga 300 a wani hari da suka kaddamar a jihar Katsina mai suna Operation Hadarin Daji.

Sadiq ya shaidawa manema labarai yayin ziyarar gani da ido da ya kai jihar ta Katsina cewa, tun a farkon wannan shekara ce aka kaddamar da shirin kakkabe 'yan bindigar daga yankin arewa maso yammacin kasar.

Ya yi kira ga 'yan bindigar, da su ajiye makamansu su kuma fuskanci shari'a. A hannu guda kuma ya bukaci sojojin, da kada su ragarma duk wani 'dan bindiga da ya ki yin saranda, ta yadda manoma za su koma gonakansu don noma abincin da za su ci da iyalansu.

A wani labarin kuma, mai magana da yawun sojojin kasa na Najeriya John Enenche, ya shaidawa 'yan jaridu a Abuja, fadar mulkin Najeriyar cewa, manufar shirin kakkabe 'yan bindigar na hadin gwiwa a jihar ta Katsina da aka fara a ranar 14 ga watan Mayu, ita ce kawo karshe matsalar da ma sauran munanan laifuka a yankin arewacin kasar ta Najeriya.

Mahukuntan Najeriyar dai sun sha kaddamar da hare-hare da ma yin sulhu da 'yan bindigar, a kokarin kawo karshen tashin hankalin dake faruwa a yankin da ya shafe shekaru yana fama da matsalar tsaro masu nasaba da fada tsakanin al'ummu kan gonaki, da hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai da kashe-kashen ramuyyar gayya daga kungoyin 'yan banga.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China