Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci birnin Wuhan da ya inganta matakan kula da wadanda suka warke daga COVID-19
2020-06-04 10:22:53        cri
Wata kungiyar masu sa-ido kan yaki da COVID-19 ta hukumar gudanarwar kasar Sin, ta shawarci mahukuntan birnin Wuhan na lardin Hubei dake yankin tsakiyar kasar Sin da cutar COVID-19 ta bulla, da su kara daukar matakan da suka dace a fannin kandagarki da hana yaduwar cutar, da ma yadda suke kula da marasa lafiyan da suka warke daga cutar.

Kungiyar ta ce, ya kamata birnin ya kara zage damtse kan aikin gwaje-gwajen da yake yi a wasu muhimman wurare, kana ya karfafa amfani da matakan kimiya da tsarin kula da wadanda suka kamu da cutar suka kuma wartke ba tare da nuna alamu ba.

Bugu da kari, kungiyar ta ce, ya kamata a rika bibiyar marasa lafiyan da suka warke daga wannan cuta, da tsugunar da su ba su shawarwari.

Rahotanni na cewa, daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yunin wannan shekara, mahukuntan birnin sun yi nasarar yiwa mutane kimanin miliyan 10 gwajin cutar COVID-19. Kuma tun fara wannan shiri ya zuwa yanzu dai, ba a samu rahoton ko da mutum guda da ya kamu da cutar ba, amma an gano tare da killace mutane 300 da suka kamu da cutar suka kuma warke ba tare da nuna wasu alamu ba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China