![]() |
|
2020-06-15 09:55:29 cri |
Ali Mohamed, kwamandan runduna ta 43 ta sojojin kasar Somali, ya fadawa 'yan jaridu cewa, sojojin sun kaddamar da mummunan harin ne bayan samun bayanan sirri daga wajen alumma.
Mohamed ya ce, an kaddamar da harin ne a garin Afmadow bayan musayar wuta tsakanin sojojin da mayakan kungiyar inda sojojin suka yi galaba kan mayakan masu tsattsauran ra'ayi, inda suka kashe 13 daga cikinsu wanda ya kunshi har da wasu manyan kwamandojin kungiyar uku.
Ya kara da cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kwato makamai daga hannun mayakan a lokacin musayar wutar.
Wasu mazauna yankin sun shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an yi mummunan artabu a kauyen Banka Jira.
A cewar Hindi Aden, wani mazaunin yankin, sun ji mummunar karar harba makamai a lokacin da sojojin suka kaddamar da hari kan mayakan al-Shabab a kauyen. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China