Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi gargadi game da barazanar bukatar agajin jin kai a Somalia
2020-06-03 10:58:16        cri
MDD ta yi kira ga kasashen duniya, su taimakawa Somalia kaucewa fuskantar manyan matsalolin jin kai saboda tasirin ambaliyar ruwa da farin dango da kuma COVID-19.

Shugaban ofishin kula da ayyukan agaji na MDD a Somalia, Justin Brady, ya yi gargadin samun koma baya dangane da nasarorin da aka samu a kasar a baya-bayan nan, a fannonin tsaro da harkokin siyasa, idan ba a gaggauta daukar matakan kaucewa aukuwar matsalolin ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a Mogadishu, Justin Brady, ya ce ana fuskantar matsalolin ambaliya da COVID-19 da suka hadu suna tasiri kan al'umma, sannan kuma ga matsalar farin dango.

Sanarwar ta ce ana sa ran samun asarar amfanin gona a bana saboda shigar farin dango, lamarin da zai kara ta'azzara yanayin rashin isasshen abinci tsakanin jama'a da dama na kasar.

Jami'in ya ce dabarun kasar na shawo kan lamarin, bai kai na kasashen dake makwabtaka da ita karfi ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China